DURUM BABBAN MOTSI: Shiekh JINGIR Yayi Kira Ga Gwamnati da ta Mayar da TALLAFIN MAI
Daga Wakilin Mu Sadiq Amsy
Fadilatu Ash-Sheikh Muhammad Sani Yahaya JINGIR, Shugaban Majalisar Malamai JIBWIS NHQ JOS Na Kasa da Kasa
Yayi Kira ga Gwamnatin Najeriya da ta Mayar da Tallafin Mai Don Talakawa Su Sami Saukin Rayuwa.
Kuma Yakara da Kira da Gwamnati da ta Biyawa Ma'aikata Alkawarin da Suka dauka musu, Don Cika Alkawari addinine.
Sanan Sheikh JINGIR Yayi Kira ga Ma'aikata da Sauran Al'umma kar su dauki hanyar Zanga Zanga A Matsayin maslaha.
Daga Karshe Sheikh JINGIR Yayiwa Kasar addu'ah Allah ya zaunar da ita lafiya.
Jibwis National HQ Jos -Nigeria
Monday 19th February 2024
0 Comments