Home Tafsir Muhadhara Nasiha Videos Khuduba Biographies News Quran Anashid

KIRA ZUWA GA YAN KWAMITIN MEDIA NA WANNAN KUNGIYAR

ASH SHEIKH SANI YAHAYA JINGIR by Saadu Ukasha 

KIRA GA ÆŠAUKACIN YAN KWAMITIN INTERNET TA KASA DA KASA (MEDIA) JIBWIS NHQTRS, JOS

ASSALAMU ALAIKUM: Muna kira ga duk wani dan Media da ke karkashin Internet Media, muji tsoron Allah Muyi rubutu Wanda zai Kawo Maslaha ga Al'ummar Musulmi.

Sannan Mu sani babu wani da aka wakilta shi yin Wani rubutu don cin mutuncin Wani Cikin daukacin wannan tafiya ta Alkhairi.

Idan wasu suna rubutun da bai dace ba kada mu maida martani wajen cin mutuncin Kowa,
Mu tsaya wajen yaÉ—a addini tare da rubutu mai ma'ana wanda duk ya karanta zai fahimce mu Kuma ya Karu da abinda Muka rubuta.

Mu Zama masu da'a bisa wannan Ummarni.
Lallai mu sani duk Abinda muka rubuta za'a tambaye mu ranar hisabi Kuma lallai mu sani Allah baya zaluntar bawa.

Ba lallai bane sai mun tankawa duk wani da yake nufin Kawo husuma a wannan tafiya Mai Albarka, 

Don Allah Muna Jayo hankalin duk Wani dan Media a matakin kasa. Jihohi. Har zuwa ƙananan hukumomi bamu yarda wani yayi rubutu don cin zarafin wani ko wasu ba.

In zamu yi rubutu muyi shi don anfanar da mutane. 

Mu sani aikin mu shine yaÉ—a da'awa ta hanyar dauko karatuttukan Iyayen mu Maluma da kuma yin rubutu a kan ilimi.

Daga ƙarshe Muna kira da muyi hattara Kuma mukai zuciya Nesa domin yan'uwantakan musulunci tafi ƙarfi kan dukkanin Wani yan'uwantaka da aka gina ta don muzantawa Musulmi da Musulunci.

Allah muke Roko kada Ya kamamu da laifin Masu wauta cikin mu, Ya ƙara mana haɗin Kai da son Juna domin neman Yardan sa.

Sanarwa Daga Sakataren yada labarai na wannan kwamiti. 
Hon.Rabiu B. Goro.

Post a Comment

0 Comments