Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, an haife shi ranar Juma’ar karshen watan Ramadhan na shekara ta 1343 ko 1345 Hijiriyya, wanda ya yi daidai da 1922 ko 1923 Miladiya, a garin Gumi a karamar hukumar Gumi cikin jihar Zamfara a tarayyar Nijeriya.
Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya ba da gudummawarsa a fagen ilimi da ilimantarsa.
Kadan daga wallafaffun littafansa akwai littafi mai suna Nazamul Kadidatu Lamiya wacce ya yi don ta’aziyyar Abdullahi Bayero Sarkin Kano.
Da wata kasida ta Kafiya wacce ya yi ta a lokacin da yake dalibta a kasar Sudan mai baitoci 34.
Kuma ya yi tafsiri mai Suna RADDUL-AZHAN ILA MA’ANIL-KUR’AN, da kuma littafinsa mai suna AKIDATUSSAHIHATBI MUWAFAKATUS SHARI’A wanda shi ne ma muka fassara a cikin wannan littafin.
Da kumalittafinsa mai suna WURDINL-AZIM MINAL KUR’ANIL KARIM WAL-AHADISIL SHARIF.
Haka kuma akwai Tarjamar Al-Kur’ani Zuwa Harshen Hausa. Da kuma Tarjamar littafin Arba’una Hadis, zuwa harshen Hausa. Da kuma Tarjamar littafin Usuluddeen da Tauhid zuwa harshen Hausa, da kuma wani littafi maisuna Mir’atul Dullab Fee Masnadil Abwab, da dai sauransu.
Kuma ya fassara wasu littattafai masu yawa a cikin kasakasai da sidi da DVD kamar irin su Ahdari, Ashmawi, Iziyya da Risala da Mukhtasar Halil da Bukhari da Fatahul Majid da sauransu.
Kuma ya sami kyauttuka na girmamawa a lokacin rayuwarsa kamar Malamin nan mutumin Siriya (Sham) mai suna Shaikh Sa’ad Yaseem-Assuri, wanda Malam (Sheikh Abubakar Mahmud Gumi) ya koyi karatun Kur’ani da Tajwid a wurinsa ya ba shi Shahada, da kuma Firimiyaan Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakwato ya ba shi lambar yabo saboda da shi ne mai yi masa tarjama in ya je kasashen Larabawa a lokacin da yake raye.
Kuma Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ba shi lambar girmamawa ta kasa mai suna (C.F.R), haka kuma Jami’ar Islamiyah da ke Madina a kasar Sa’udi Arabiya ta sa shi daga cikin Malamai masu ba ta shawara har sau uku. Haka nan mai girma Jamal Abdulnasir wanda yake shugaban hadin kan kasashen Larabawaa lokacin da yake mulki, ya ba shi takardar girmamawa saboda yada addinin Musulunci a duniya.
Haka kuma Malik Faisal na kasar Sa’udi Arabiya ya ba shi takardar girmamawa saboda yada addinin Musulunci da ya yi a duniya.
Wadannan kadan ne daga cikin irin girmamawar da Allah ya yi masa.
RASUWARSA
Sheikh Abubakar Mahmud ya rasu ranar Juma’a 11 ga watan 9 a shekarar 1992, sakamakon rashin lafiya.
Shugabanni da yawa sun halarci Jana’izar sa wanda aka yi a garin Kaduna, kamar su shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida, da Ministoci da Sarakuna da Talakawa na kasar nan da kuma ketare.
0 Comments