Home Tafsir Muhadhara Nasiha Videos Khuduba Biographies News Quran Anashid

Sheikh Isma’ila Idris bn Zakariyya






Sheikh Isma’ila Idris bn Zakariyya ya taso ne cikin al’umar nan tamu ta Nigeria, a yankin Arewa inda a wannan lokacin babu wata akida a kasar nan bayan Dariqar Tijjaniyya, karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Inyas Alkaulahy.

To da yake zamani ya nausa tafiya tayi nisa, Al’umma ta samu kanta cikin yanayi na cakuda addini da son zuciya. Ana samun malamai masu sanya son ransu a cikin addini suna amfani da sunan addini suna isar da munanan manufofinsu ga al’umma kamar bokanci da sihirin duba da ma wasu tsubbace-tsubbace su na son zuciya da neman duniya.

    Wanda ya ci karo da koyarwar Addinin Musulunci. Dukkan mai irin wadannan aiki bai taba yin su ba face sai ya fita daga addinin Musulunci, Ya zamo dukkan wanda yayi Sunansa kafiri da Nassin Aya acikin Suratu baqarah. Haqiqah bayan Wannan Akwai wasu littattafai dadama wadanda Maluma suka shigo dashi ake karantasu na Labaran mafarki da Tatsuniyoyi dasunan Adddini, Irin wadannan abubuwa dakuma makamantansu Sune maqasudin Da’awar ta Sheikh Isma’il Idris, a bisa fahimtar masu kyautata masa zato.


    Da’akwai wadanda suke ganin cewa kawai yafara da’awar izala ne kawai Don Neman Suna dakuma Zagin Wasu malamai (Shehunnan ‘Dariqu) da kuma Sufaye. Wanda kuma hakan kuskurene domin  Aikin Musulmi shine kyautatawa juna zato. Da Kuma nemawa juna gafara a gun da aka yi kuskure dangane da sa’banin ra’ayi ko fahimta.
   
    Bayan Malam ya bar aikin Soja wanda a cikin aikin nasa na soja ya fara da’awa akan barin tsubbu da daura layu da makamantansu, Malam ya sha tsangwama daga makiya da kuma wadanda basu da ilimi wanda basu fahimce shi ba. A wannan Lokaci malam ya gane cewar wannan da’awa tasa ba zata cigaba ba Har sai da wata kungiya wacce zata tallafa masa dangane da samun cikar kudirinsa na farkadda mutane game da sunnah ta asali.


    A wannan lokaci ne malam ya assasa wata kungiya mai Suna; ”Jama’atu izalatul Bid’ah ” Ma’ana ( Kungiyar dake kawar da Bidi’ah ) Wannan kungiya tasa ta samu karbuwa hatta a cikin ‘yan uwa sojoji na wannan lokaci, sai dai kuma ta samu nakasu sosai daga Malaman wannan zamanin musamman wadanda keda Wannan akidar ta tsubbace-tsubbace da duba. Ta yadda suka yita yi masa tuggu da zagon kasa wurin sun ga sun dakushe wannan aikin nasa, tare da wargaza aikin nasa ta hanyar kirkiran karya akansa hadda cutar da shi domin su samu galaba akansa, amma a hakan Allah ya tseratar da shi daga dukkan tarkunan nasu Allah Ya kuma karfafa wannan da’awa tasa har ilayau kugiyar Izala tana nan kuma tana cigaba da aikinta wajen karantar da al’umma bisa koyarwar magabata da kuma tabbatar da Qur’ani da Hadisi sune tafarkin tsira ga bayi.


    A hakan aka cigaba da kasancewa har ta kai yaje izuwa ga Malaminsa na Tauhidi Assheikh Abubakar Mahmud Gumi, Domin neman izini da Karin lamani dangane da Da’awar tasa. Awannan lokacine Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya kuma Bashi cikakken goyon baya gami da cikata masa Sunan kungiyarsa da ” Wa’iqamatis sunnah ”  ma’ana ( Da kuma Tsayar da Sunnah ) Wacce ta zamo ” Jama’atu izalatul Bid’ah Wa’iqatissunnah ” Ma’ana ( Kungiyar dake kawar da Bidi’a kuma take Tsayar da Sunnah ) domin a cewarsa Sheikh Abubakar Mahmud Gumi; Babu yadda za’a yi a kawar da bidi’a a barta haka ba a cike gurbinta da wani abu ba, shine yace to sai a cike gurbinta da sunnah.

    


Post a Comment

0 Comments