Home Tafsir Muhadhara Nasiha Videos Khuduba Biographies News Quran Anashid

Sheikh Sani Yahaya Jingir


 Sheikh Sani Yahaya Jingir Malamin Addinin Musulunci ne da ke zaune a Jihar Filato, Shi ne Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa, Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa’Ikamatis Sunnah JIBWIS ta bagaren Jos.

A shekarar 2000 an zabe shi a matsayin shugaban majalisar lokacin da aka yanke hukunci bayan taron majalisar a Jos wanda majalisar dattawan Ulama’u ta yi. An yi zaben ne lokacin da majalisar ta rasa shugabanta Sheikh Zakariyya Balarabe Dawud.

Jingir yana gabatar da tafseer na Ramadan na shekara shekara a Jos, yana daya daga cikin fitattun malamai a Arewacin Najeriya. Jingir yana wa’azin koyarwa kan muhimmaci da fa’idar bayar da ilimi a tsakanin ‘ya’yan maza da mata.

Jingir yayi wahalar yin wa’azi musamman ga yan Boko Haram ta hanyar cewa aikin su na ta'addanci bai dace da Shari’ar Musulunci ba. Jingir a lokacin bude masallacin Juma’a da ke saman tudun Zinariya a Arewacin Jos, ya gargadi masu garkuwa da mutane a fadin kasar nan da su nemi gafarar Allah, su kuma tuba, idan kuwa ba haka ba zai shirya addu’o’i da azumi na musamman har sai Allah Ya halaka su.

Post a Comment

0 Comments